Ba Ni Tabbacin Har Yanzu Jonathan Na PDP – Sule Lamido

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa a wata tattaunawa da sashin Hausa na BBC ya yi da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido kuma jigo a jam’iyyar PDP an tambaye shi idan har yanzu Jonathan dan jam’iyyar PDP ne.

Sai dai amsar da Sule Lamiɗo ya bayar ba tazo da mamaki ba “Ina tantamar hakan, ya jima ba ya shiga al’amuran jam’iyyar da ake gudanarwa kwanan nan.”

Haka zalika, Lamido bai yi nauyin baki ba yayin da shugabannin jam’iyyar PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ziyara, inda ya ce, sun zo ne don su nemi mafita mai dorewa ga matsalolin da kasar ta ke fuskanta.

“Tun lokacin da Buhari ya amshi mulki, Najeriya ba ta kara samun natsuwa ba saboda gwamnatin ta tarwatsa duk matakan da PDP ta kawo na cigaba. “Ba mu da kwanciyar hankali, hadin kai, daraja, rikon amana kuma akwai tabbataccen talauci, saboda haka muna so mu canza wadannan abubuwan.

Shiyasa muka yanke shawarar mu zo mu samu Obasanjo don yin hakan. Mun kai a kalla awa biyu muna tattauna wa da shi.”

Labarai Makamanta