Fitaccen jarumi a Masana’antar fina-finai ta Hausa kannywwod, Sule Yahaya Hamma wanda aka fi sani da Sulaiman Bosho ya ce shi a duk cikar masana’antar da batsewar ta ba shi da wani Uban gida, wanda zai ce shi ne ya koya masa harkar fim.
Jarumin ya bayyana Hakan ne a yayin tattaunawar su da jaridar Dimukaradiyya in da ya ke cewa.
“Ni harkar fim din nan da Ni aka fara ta ina cikin ta wajen shekaru 30 Kenan, don haka ba Ni da Uban gida a cikin ta, idan kuma wani ya ce shi ne ya koya mini, to ya fito ya fada. Amma dai Ni na san ba Ni da Uban gida a cikin harkar fim Ina cikin ta ne tun farkon kafuwar ta. ”
Dangane da burin da ya ke da shi a game da harkar fim kuwa cewa ya yi.
” A gaskiya buri na shi ne mu yi amfani da fim wajen isar da kyawawan dabi’u na Musluci da Kuma al’adun mu a duniya, don haka ina alfahari da harkar saboda sana’a ta ce wadda ta rufa mini asirin.
” Don mun samu arziki a cikin ta na yi aure na yi motoci Kuma da ita mu ke ciyar da iyalan mu har ma mu ke yi wa mutane alheri da abun arzikin da mu ke samu,” acewarsa
You must log in to post a comment.