Ba Nauyin Gwamnatin Tarayya Ne Hukunta ‘Yan Bindiga Ba – Mohammed

Ministan Yaɗa Labarai na Najeriya Lai Mohammed ya nemi jam’iyyar adawa ta PDP da ta tuhumi gwamnonin ƙasar game da rashin hukunta ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane da aka kama maimakon gwamnatin tarayya.

A cewar ministan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, alhakin hukunta masu aikata fashi da kuma garkuwa da mutane ba na gwamnatin tarayya ba ne.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman da ya ce PDP ta yi tana mai sukar gwamnatinsu ta APC game da matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar a nata taron manema labaran na ranar Litinin.

“PDP ta yi zargin cewa ba a gurfanar da ‘yan fashi a gaban kotu…abin mamaki ne a ce jam’iyyar PDP da ta mulki ƙasar nan tsawon shekara 16 ba ta san cewa hukunta masu fashi da garkuwa da mutane ba haƙƙin gwamnatin tarayya ba ne,” in ji shi.

“Saboda haka, ya kamata PDP ta matsa wa jihohi da kuma gwamnoni domin tabbatar da cewa an gurfanar da ‘yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane da aka kama.”

Tun farko PDP ta nemi Shugaban Ƙasa Buhari ya kafa dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a ƙasar baki ɗaya sakamakon kashe-kashen da ‘yan fashi da Boko Haram ke aikatawa a arewaci da kuma masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya a kudanci.

Ministan ya zargi PDP da “yin wasa da kuma siyasantar da matsalolin ƙasa”.

Labarai Makamanta