Ba Na Shakkar Kowa A Kannywood – Jaruma Hussaina Musa


“Duk a cikin Matan Kannywwod a yanzu babu wata jaruma da ne ke ganin za ta shiga gaba na da za a ce za ta yi wani abin da ni ba zan iya yin sa ba, domin kuwa a yanzu nima lokaci na ya zo a na damawa da ni”.

Wadannan kalaman sun fito ne daga bakin jaruma mai tasowa Hussaina Musa, wadda ta fito a matsayin Samira a cikin fim Mai dogon zango na Izzar so, a yayin tattaunawar ta da Jaridar Dimukaradiyya.

Jarumar wadda ta Dade a cikin Masana’antar, Sai dai ba ta samu damar da tauraruwar ta take haskawa ba Sai a yanzu da take taka rawa a cikin Izzar so din, don haka take ganin a yanzu karanta ya kai tsaiko.

“Ni a yanzu ba na shakkar kowa in dai a cikin harkar fim ne, saboda na Dade a cikin harkar na ga duk wasu abubuwa da suka sameni na darasi, don haka idan Mace ta na ganin ta iya aikin to nima na iya, idan rawa za ta yi a kalle ta, to nima na iya idan har ban fi ta ba, to ba za ta fi ni ba.

Ta ci gaba da cewa” Ni ba na rigima da kowa muna zama da kowa lafiya, don haka tun da na shigo harkar fim ba ni da abokin fada duk Ina kallon kowa a matsayin abokan sana’ar da na ke yi don haka duk abu daya ne. ”

Daga karshe ta yi fatan Allah ya sa ta Gama da harkar fim din lafiya, ta samu miji ta yi aure kamar yadda sauran Mata su ke yin aure su ke zama a dakin mijin su tare da ‘ya’yan su.

Labarai Makamanta