Ba Na Goyon Bayan Muƙabalar Abdul-Jabbar Da Malaman Kano – Dr Gumi

Mashahurin Malamin addinin Musuluncin nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya bayyana cewar ko kaɗan baya goyon bayan zaman muƙabala tsakanin Abdul-Jabbar da malamai da gwamnatin Jihar Kano ke burin yi.

Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da karatun Siyasa Al- Shar’iyya da ya saba gabatarwar a babban masallacin juma’a na tunawa da Marigayi Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake Unguwar Sarki Kaduna.

Babban Malamin ya bayyana cewar Mukabala ko Munazara ana yin su ne a tsakanin Malamai da niyyar fito da gaskiya akan abin da ya shige wa juna duhu.

Dr. Gumi ya ƙara da cewar ba a gudanar da muƙabala tsakanin Malamai da Jahilai ko a gaban Jahilai, dalilin kuwa mai baki a cikin muƙabalar zai iya galaba ta hanyar ɗaga sauti har Jahilan Mutane su ɗauka cewa shi ke da gaskiya kuma ya yi galaba.

“Ina kira da babbar murya ga Malaman Jihar Kano da su kauracewa wannan zama da za’a yi, domin ba zai haifar da natija ba illa ya kunno wata sabuwar fitina”.

Dr. Gumi ya ƙara da cewar, abin da ya tabbata shine Abdul-Jabbar dai ɗan Shi’a ne mai da’awa akan Shi’anci, saboda haka babu dalilin da Malaman Sunnah za suyi zama da shi akan littafan Sunnah, sai dai in zai zamana zai dauko littafan Shi’a ne su kuma Malamai su zo da littafan Sunnah, matuƙar ba haka ba babu dalilin da zai sa ayi zama da ɗan Shi’a akan littafan Sunnah.

Labarai Makamanta