Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, CAN, ta yi watsi da matakin gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa’i na rage kwanakin aiki ga ma’aikatan gwamnati daga biyar zuwa hudu.
A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da wannan mataki, wanda ta ce zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disambar shekarar da muke ciki.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Rabaran Joeshep Hayaf ya aike wa manema labarai a ranar Talata, CAN ta ce kada ma’aikatan gwamnati su yadda da wannan batu, domin kada a yi musu sakiyar-da-ba-ruwa sai nan gaba a fito da wani abu da ba su san da shi ba.
”Ta yaya jihar da ke fama da matsalar tsaro, za a zo ace wai mutane su koma gona, alhalin gonakin a wajen gari suke, Mai zai faru idan su na gonar ‘yan bindigar suka far musu a gona, ko kuma aka shiga gidajensu?
Ma’aikata su tabbatar ba wani salo aka bullo da shi, sai nan gaba a shayar da su mamakin an rage musu albashi tun da ba aikin kwanaki biyar a mako kamar yadda aka bisa al’ada ake yi,” in ji Hayaf.
You must log in to post a comment.