Ba Mu Yarda A Yaki ‘Yan Bindiga Da Jiragen Da Muka Sayar Ba – Amurka

Rahotanni dake shigo mana daga Hedkwatar tsaro ta ƙasar Amurka na bayyana cewar gwamnatin kasar ta yi zazzafan gargadi ga gwamnatin tarayya akan amfani da jiragen yaƙin da ta sayar mata wajen kai wa ‘yan Bindiga waɗanda ke addabar yankin Arewa maso yamma farmaki.

Tun bayan isowar jiragen Najeriya a watan Yuli bayan kammala ciniki, ƴan ƙasar da dama sun saka ran cewa nan da nan za a fara amfani da su wajen kai wa ƴan fashin daji hare-hare don murƙushe su, musamman a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Sai dai rahotanni sun ce akwai wani babban lamari da ke jawo tsaiko wajen aiwatar da hakan, wanda bai wuce sharaɗin da ke dabaibaye da sayen jiragen ba tun farko, wanda Amurka ta sanya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta shaida wa Majalisar Dokokin ƙasar cewa, tun farko Amurka ta yarda ta sayar da jiragen yaƙi na A-29 Super Tucano 12 ne idan za a yi amfani da su a kan ƴan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya ne kawai, ban da ƴan fashin daji.

Labarai Makamanta