Ba Mu Janye Tuhumar Da Muke Yi Wa Tukur Mamu Ba – DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta rahoton da ke yawo cewa ta janye ƙarar data shigar kan Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakani da ‘yan ta’adda.

Wani rahoton da ake yaɗawa ya yi ikirarin cewa hukumar ta janye ƙarar da ta shigar a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, inda ta samu sahalewar tsare shi na kwana 60.

Rahoton ya nuna Lauyan DSS, A. M Danlami ya shaida wa Mai shari’a Nkeonye Maha, jim kaɗan bayan kiran ƙarar, cewa hukumar ta jingine shari’ar.

Amma a wata hira da jaridar Daily Trust ranar Alhamis da daddare, mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana rahoton da, “Karya mara tushe.”

Mista Afunanya ya jaddada cewa DSS ba ta janye ko tuhuma ɗaya da take wa Tukur Mamu ba, inda ya bayyana cewa lamarin wani batu ne da za’a cigaba da shi.

Idan baku manta ba a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, Jami’an tsaro suka kama Mamu a Cairo, babban birnin ƙasar Masar lokacin yana tare da iyalansa.

Mamu, fitaccen ɗan jarida a Kaduna kuma makusancin Shahararren Malamin Nan, Sheikh Ahmad Gumi, shi ya shiga tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna.

Labarai Makamanta