Ba Mu Dakatar Da Samar Da Iskar Gas Ba – NLNG

Kamfanin samar da iskar gas na girki a Najeriya, Nigeria LNG Limited (NLNG), ya musanta rahotannin da ke cewa ya dakatar da aiki a wasu masana’antunsa da ke kudancin ƙasar saboda ambaliyar ruwa.

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter, NLNG ya ce dukkan masana’antunsa na aiki “duk da cewa ba yadda suka saba ba saboda ƙarancin gas da yake fuskanta daga abokan hulɗarsa”.

Tuni aka shiga fargabar hauhawar farashin gas ɗin saboda tsoron ƙarancinsa a kasuwa bayan kamfanin ya ba da sanarwar rage yawan gas ɗin da yake samarwa saboda raguwar da aka samu daga abokan hulɗarsa da ke samar masa da ɗanyen gas, wanda ambaliyar ta haifar.

“Babu wata masana’antarmu a Tsibirin Bonny ko kuma wani wuri da ta fuskanci matsala sakamakon ambaliyar ruwa,” a cewar kamfanin.

NLNG ya ce yana ci gaba da samar wa kasuwar cikin gida gas ɗin daga abin da yake da shi a rumbunsa kuma yana ci gaba da lalubo hanyoyin magance matsalar da ambaliyar ta haifar wa abokan hulɗar tasa.

Labarai Makamanta