Ba Mu Dakatar Da Kwankwaso Ba – PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta musanta wata takarda da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke cewa jam’iyyar ta dakatar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da takwaransa Babangida Aliyu na jihar Neja.

Cikin wata sanarwa da PDP ta fitar a shafinta na Twitter ta ce, akwai wasu ka’idoji da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada gabanin dakatar da duk wani mamba.

PDP ta ce ba za ta amince da irin wadannan karyace-karyacen ba, wadanda za su iya kawo hargitsi cikin jam’iyyar ko kuma su haifar da rikici tsakanin mambobinta.

Haka kuma ta musanta dakatar da tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu tana cewa duka bayanan da aka fitar na dakatar da shi basu da tyshe bare makama.

Jam’iyyar ta shawarci shugabanninta a jihohin Kano da Neja da su hada kai wuri guda su kuma yaki irin wadannan bayanan da za su iya kawo rabuwar kai, a lokacin da ‘yan Najeriya ke bukatar jam’iyyar.

Labarai Makamanta