Ba Mu Da Wani Shiri Na Fasa Gudanar Da Zaben 2023 – INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya jaddada shirinsu na gudanar da babban zaɓe na 2023 a lokacin da aka tsara, yana mai cewa “ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen ba”.

INEC ta tsara gudanar da zaɓen daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za a zaɓi shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya, daga baya kuma a zaɓi gwamnoni da ‘yan majalisar jiha a watan Maris.

Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami’in Inec ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro za su sa a ɗaga zaɓen a wasu yankunan Najeriya.

“Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin zaɓen ballantana ma ɗage shi. Irin tabbacin da jami’an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma’aikatanmu ya ƙarfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu,” in ji farfesan a ranar Laraba.

Ya ba da tabbacin ne yayin da ya gana da jam’iyyun siyasa 18 da za su fafata a zaɓen, inda ya gabatar musu da kundin rajistar masu kaɗa ƙuri’a da yawansu ya kai miliyan 93.4.

“Babban zaɓen 2023 zai gudana yadda muka tsara shi. Duk wani rahoton da ya ruwaito saɓanin haka ba matsayarmu ba ce,” kamar yadda ya jaddada.

Labarai Makamanta