Ba Mu Da Niyyar Sayar Da Kamfanin Dillacin Wutar Lantarki – Gwamnatin Tarayya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ce ba ta da niyyar cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasar.

Rahotanni sun bayyana hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, in da ta bukaci jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke cewa za ta yi hakan.

Wannan dai martani ne ga rahotannin kafafen yada labarai da ke bayyana cewa gwamnati na shirin cefanar da kamfanin, inda rahotannin suka ce za a yi hakan cikin watanni masu zuwa.

”Gwamnatin tarayya ba ta da shirin sayarwa ko kuma cefanar da kamfanin dillancin wuta na kasa, kuma babu wani daga gwamnatin da ya sanar da hakan,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin tarayya karkashin mulkin shugaba Buhari na mayar da hankali kan zamanantar da bagaren wutan lantarki na kasar ta hanyar bijiro da tsare-tsare wanda ya hada da hadin gwiwa da shirin inganta wuta na ofishin shugaban kasa.

Labarai Makamanta