Ba Mu Da Hannu A Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Talauci – Gwamnoni

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin Najeriya 36 sun ce sun yi mamakin yadda ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na ƙasar, Clem Agba ya zarge su da jefa Najeriya cikin talauci.

A watan Nuwamba ne Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce mutum miliyan 130 ne a ƙasar ke fama da talauci, kusan kashi 63 cikin 100 na a’umar ƙasar.

To sai dai a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo, ta bayyana kalaman ministan da cewa abu ne da bai kamata ba, kuma babu kanshin gaskiya a cikin kalaman ministan.

Gwamnonin sun ce iƙirarin – da ministan ya yi cewa gwamnonin sun yi watsi da al’ummar karkara – ba shi da tushe balle makama.

A cikin makon da ya gabata ne dai ƙaramin ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare Clem Agba a wani taro da ya yi da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ya ɗora alhakin katutun talaucin da ke damun ƙasar kan gwamnonin jihohi.

Labarai Makamanta