Ba Gaskiya Bane Labarin Boko Haram Sun Shiga Abuja – Rundunar ‘Yan Sanda

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan babban birnin ta musanta rade-radin da ake yi na cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki babban birnin kasar na Najeriya.

Ana ta yadawa cewa Boko Haram sun kai hari Abuja bayan samun su da aka yi a jihar Neja dake makwabtaka da babban birnin na Abuja.

Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ta ce an ga jama’a masu yawa a babura a wasu sassan babban birnin tarayyan, lamarin da ya kawo wannan rade-radin kuma yasa jami’ansu suka fita sintiri.

A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, Mariam tace an fara tsananta sintiri kuma hakan yana daga cikin matsayar da aka cimmawa bayan taron hadin guiwa na jami’an tsaro da aka yi a ranar Alhamis.

“Hankalin jami’an tsaron hadin guiwa na babban birnin tarayya ya je kan wata wani labari dake yawo wacce tace miyagun ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hari babban birnin tarayya.

“Jami’an tsaron hadin guiwan na sanar da cewa babu gaskiya a cikin wannan labarin kuma an yi shi ne domin gigita jama’a mazauna babban birnin tarayyan. “Akasin wannan hasashen, shugabannin cibiyoyin tsaro na babban birnin tarayyan sun tashi domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi garin kuma hakan yasa suka yi taro a ranar Alhamis, 29 ga watan Afirilun 2021.

“Kungiyar ta yanke hukuncin tura jami’an sintiri yankunan da matsalar tsaron ta fi addaba. “Hukumomin tsaron sun fara aiki da babura, dawaki da sauran hanyoyin samo bayanai domin bankado dukkan matsalar tsaro a babban birnin.”

Bala Ciroma, kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya yayi kira ga mazauna birnin da su kwantar da hankulansu sannan su kasance masu kiyaye doka.

Labarai Makamanta