Ba Gaskiya Bane Bidiyon Karbar Dalar Ganduje- Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sake jaddada cewa bidiyon da ya bayyana a 2018 yana cusa dalolin Amurka cikin aljihunsa sharri ne kuma na boge ne, kuma tabbas zai ɗauki matakan da suka dace akai.

Jaridar Daily Nigerian a 2018 ta wallafa bidiyoyin kuma hakan ya yi matukar batawa gwamnan suna.

Bayan shekaru biyu Gwamna Ganduje ya bada amsa kan wannan lamari a shirin BBC Hausa “A fada a cika” wanda gidauniyar MacAuthur ke daukar nauyi.

Ganduje ya ce bidiyon na bogi ne kuma “wadanda suka yi za su ji kunya.”

“Babu shakka wannan bidiyo karya ne kuma muna nan muna shirye-shirye amma ba zamu fadi irin shirin da muke ba…duk wadanda suka sa hannunsu a wannan lamari za su ji kunya,” cewar Ganduje.

Tun bayan bayyanar Bidiyon a shekarar 2018 wanda Kamfanin jaridar Daily Nigerian ta fitar jama’a ke ta faman yin tsokaci da cece kuce akai.

Majalisar dokokin Jihar Kano ta gayyaci mawallafin jaridar mai suna Jaafar Jaafar inda ya bayyana gabanta rataye da gafakar Kur’ani sannan ya yi rantsuwa akan sahihancin faifan bidiyon.

Labarai Makamanta