Ba Dole Bane Tinubu Ya Rinka Halartar Zaman Mahawara – APC

A cikin wata sanarwa da Kwamitin yakin neman zaben Tinubu ya fitar ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya bai wajabtawa dan takararta halartan muhawarar da wata kungiya ta shirya ba, saboda haka ba dole bane.

A wata sanarwa da Arise TV ta fitar kwanan nan ta bukaci dukkan ‘yan takarar da su mutunta kundin tsarin mulkin kasar kuma su halarci muhawarar da ta shirya.

“Muna tsammanin duk ‘yan takarar da ke neman zabe kuma su kafa gwamnati a karkashin wannan tsarin mulki, ya kamata su mutunta doka, tare da halartar tarurrukan muhawara da kafafen yada labarai suke shiryawa” in ji sanarwar da Arise TV ta fitar.

Tinubu ya ki amsa gayyatar Muhawarar a karon farko wanda aka shirya kan tsaro da tattalin arziki a ranar 6 ga watan Nuwamba. Ya ce muhawarar ta ci karo da jadawalin yakin neman zabensa. An maye gurbinsa da Kola Abiola, dan takarar jam’iyyar PRP sai kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu wakilcin abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

APC ta zargi gidan talabijin din da nuna son kai ga Tinubu kuma ta sha alwashin ba za ta halarci duk wata muhawara da Arise TV ta shirya ba. “Mun lura da cewa Arise News ta shirya yakin neman zaben ‘yan takarar shugaban kasa da sunan muhawarar ta hanyar amfani da sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Najeriya. “Duk da cewa ya dace kafafen yada labarai suna da aikin da kundin tsarin mulki ya ba su karara na su riga sanar da aiyukan mukaman gwamnati ga ‘yan kasa da kuma rawar da suke takawa a matsayinsu na masu sa ido ga al’umma, amma babu wani bangare na kundin tsarin mulki da sashe na 22 da ya ce dan takarar shugaban kasa ya halarci taron Arise News Town Hall ba ko duk wani taron da aka shirya a kafafen yada labarai kwata-kwata.

Kuma abinda ya hana Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zuwa wannan muhawarar shine; yana da nasa jadawalin ayyukan yakin neman zabe da sauran al’amura a ciki da wajen Najeriya. Daya daga cikin irin wannan taron shi ne taron da ya shirya yi a ranar Litinin, 5 ga Disamba, 2022 a Chatham House da ke Landan inda zai yi magana kan Tsaro, Tattalin Arziki da Manufofin alaka da kasashen waje, in ji kwamitin.

“Muna amfani da wannan damar wajen gargadin masu magana da yawunmu da magoya bayanmu da su kaucewa wannan tasha bisa rashin da’a da nuna son kai ga dan takararmu da jam’iyyarmu,” inji ta.

A watan Nuwamba,Kwamitin yakin neman zaben Tinubu ya rubuta koke ga hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBC) inda ya bukaci a kakaba wa Arise TV da sauran kafafen yada labarai takunkumi.

Labarai Makamanta