Ba Dole Bane Sai Shugaban Kasa Ya Yi Magana Akan Komai

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa idan aka ce komai sai Buhari ya fito ya yi magana, ciki har da batun rikicin Fulani makiyaya, to zai zama mai yawan surutu kenan tamkar ‘Waziri Aku.’
Adesina ya yi wannan kalami ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, a filin siyasa da ake kira ‘Politics Today’, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

Jama’a da dama sun nemi Shugaba Buhari ya fito ya yi wa Najeriya jawabi domin ya fito karara ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kashe-kashen da wasu makiyaya ke yi.

Shi ma Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya nemi a kafa dokar da za ta hana Fulani makiyaya hijira daga Arewa su na nausawa kudancin kasar nan.

Ya kara da cewa hana makiyaya karakaina cikin yankuna daban-daban na kasar nan, zai kawo karshen kashe-kashen da ake yi tsakanin makiyaya da manoma.

Da aka tambayi Adesina ko mene ne fahimtar Buhari a kan shawarar da Ganduje ya bayar, sai Adesina ya ce, “ka san idan akwai matsala irin wannan, a rika bayar da shawarwari da yawa. To amma ba lallai duk maganar da aka yi sai Shugaba Buhari ya fito shi ma ya yi bayani a koda yaushe ba.

“Ba fa sai Buhari ya rika fitowa a kullum ya na yawan magana a kan duk wani batu da ya taso ba. Sai dai a duba batun, sannan a fito da matsayar da aka cimma.

“Amma bai yiwuwa a ce duk lokacin da aka fito da wata shawara daya, sai Shugaban Kasa ya fito ya yi magana ba. Gobe kuma idan wani batu ya taso, shi ma a ce sai ya yi magana ba. Duk shugaban da zai rika yin irin haka, zai zama sarkin surutu kenan.”

Yayin da jama’a da dama ke neman a halasta wa kowa mallakar bindigar kare kan sa, Adesina ya ce shi dai Buhari ya na nan bisa abin da doka ta tanadar cewa, duk wanda aka gani da makami ba bisa ka’ida ba, to a damke shi.

Labarai Makamanta