Ba Akai Hari Mahaifar Sakataren Gwamnatin Tarayya Ba – ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta karyata raderadin da ake ta yadawa wai Boko Haram sun kai hari kauyukan Dabna da Kwabre da suke gundumar Dugwaba, karamar hukumar Hong.

Kakakin ‘yan sandan jihar Sulaiman Nguroje ya bayyana cewa wannan rahoto ba gaskiya bane yana mai yin karin bayani kamar haka ” Ko da muka ji wai Boko Haram sun kai wa wadannan kauyuka hari nan da nan muka tura zakakuman jami’an mu domin su kai dauki. Sai dai kuma isar su ke da wuya sai suka ga ashe ba gaskitya bane.

” Kowa na gudanar da harkokin sa yadda ya kamata babu fargaba ko kuma alaman an kawo hari wadannan kauyuka.

Bayan haka hakimin Dugwaba shima ya tabbatar wa Kamfanin dillancin Labaran Najeriya cewa ba a kawo hari wannan kauyuka ba duk karerayi ne kawai wasu ke kantarawa.

Dugwaba ne mahaifar sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Labarai Makamanta