Ba A Yi Wa Buhari Ihu A Jihar Katsina Ba – Rundunar ‘Yan Sanda

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar sun damke wasu matasa takwas kan zargin tada tarzoma yayinda Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara jiharsa ta Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, a ranar Juma’a yace bayan shugaban kasa ya kaddamar da titin kasan Kofar Kaura, sun samu labarin cewa wasu kauraye daga Sabuwar Unguwa na fada kuma suka fara sace wayoyin mutane.

Ya ce hukumar ta gudanar da bincike inda ta gano Kaurayen sun yi amfani da yara wajen jifan motocin jami’an gwamnati da aka tura wajen.

Gambo ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Juma’a, yace bidiyoyin da suka yadu a kafafen sada zumunta dake nuna ana yiwa Buhari ihun bamaso na bogi ne.

Labarai Makamanta