Ba A Taba Gwamnati Da Ta Cuci ‘Yan Najeriya Kamar Ta Buhari Ba – Kungiyoyi Arewa

Gamayyar kungiyoyin cigaban yankin Arewa ta bayyana cewar a tarihin Najeriya ba a taɓa samun wata gwamnati wadda ta cuci ‘yan Najeriya sannan ta raina musu hankali kamar gwamnati mai ci a yanzu ta Shugaba Buhari.

Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin Alhaji Nastura Ashir Sherif ne ya bayyana hakan, lokacin da ya ke tsokaci dangane da cire tallafin fetur da sauran kalubale da Najeriya ke ciki, a wata ganawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

Shugaban amintattun yace tun farko yaudara ce gwamnatin Buhari ta sanya akan batun cire tallafin mai, domin tuni gwamnatin ta cire duk wani tallafi na mai tun lokacin da ta ƙara farashin litar mai daga yadda ta same shi a baya.

Ashir Sherif ya kara da cewar Buhari ya jefa Najeriya cikin wani wagegen rami wanda fita daga cikin sa zai yi wahala sakamakon kazamin bashin da yake ciwowa daga waje a hannun muggan kasashe ‘yan jari hujja.

“Ina tabbatar muku a halin yanzu wannan gwamnati ta kammala dukkanin wasu shirye-shirye na sayar da titunan ƙasa, Manyan asibitocin gwamnati da Bankuna ga wasu ‘yan jari hujja waɗanda babu tausayin talaka ko na miniti guda a zukatansu”.

“Karshen al’amari shine ‘yan Najeriya za su koma bayi a kasar su a karkashin wadannan ‘yan jari hujja waɗanda ba su haura mutum 500 ba”.

Labarai Makamanta