Ba A Samun Daukaka Da Girman Kai – Jarumi Auwal Isa West


Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Auwal Isah West, ya bayyana cewar akwai bambanci sosai a tsakanin jarumai na yanzu da kuma na baya.

Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, Inda yake cewa na shafe tsawon lokaci sama da shekaru 20 a wannan masana’antar, wadda tunranda na shigo ina aikin tuka motar Tixi a lokacin ina daukar kaya idan za a tafi wajen lokeshin da haka na zo na zama jarumi don haka na sha Gwagwarmaya sosai.

Sannan kuma duk wanda ka gani iri na to da haka ya fara sai da ya Sha matukar wahala sannan ya zama wani abu sabanin wadanda su ke shigowa harkar a yanzu musamman mata wanda su burin su daga sun zo cikin harkar kawai ya za a yi su yi suna.”

Kazalika Ya ci gaba da cewa” kuma da yawan su basu da biyayya basu da girmama na gaba dasu, kawai idan kaga suna girmama ka, to wani abu suke so a wajen ka, kuma daga sun samu zasu nuna kai ba kowa ba ne a wajen su, sai su dinga ganin su kamar kai daya suke da kai, wanda a lokacin mu ba haka abun yake ba.

Wannan yasa a wannan lokacin zaka ga an yi wa yaro fina-finai ko wakoki masu yawa, amma idan ya fito gari dan kallo ma bai san shi ba, saboda ba su tsaya sun yi hakuri sun yi biyayya gana gaba dasu kamar yadda muka yi ba.

“Don haka sai ka ga mun jera dasu muna tafiya muna bayan ana kallonmu amma ba su ake kallo ba,mu ake kallo don ba a gane su ba.”

Sai dai Jaridar Dimokuradiyya ta tambaye shi har yanzu ko burin sa ya cika a masana’antar shirya fim?
Sai yace” Alhamdulillahi, za iya cewa hakan, domin ina da rufin asiri na rayuwa daidai gwargwado a matsayina na mai karamin karfi idan dan abu ya taso mun da na kusa da ni, cikin rufin asirin Allah abin baya gagara ta don haka sai godiya ga Allah.”

Daga karshe ya yi kira ga sababbin jarumai dasu rage girman kai su rinka girmama manya domin su samu daukakar da suke bukata.

Labarai Makamanta