Ba A Samu Ganin Jinjirin Watan Salla A Najeriya Ba – Sarkin Musulmi

Kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun ce ba su samu rahoton ganin jaririn watan Shawwal a Najeriya ba a yau Talata 11 ga watan Mayun 2021 wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Ramadan 1442 AH.

Don haka Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mini ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal.

Sarkin Musulmi ya taya Musulmin Najeriya murna tare da fatan Allah ya yi masu albarka.

Labarai Makamanta