Ba A Kowane Fim Nake Fitowa Ba – Sani Danja


Fitaccen jarumi a masana’antar fina-finai ta Kannywood Sani Musa Danja, ya bayyana cewar, akwai wasu abubuwa da ko nawa za a ba shi to babu yadda za a yi ya fito a cikin fim.

Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu in da ya ke cewa,

“Ni Musulmi ne kuma suna na Muhammadu Sani ka ga ai Sani Muhammadu ne sunan Musulmi ne don haka a fim da na ke yi ba zan yi abin da ba daidai ba.”

Ya Kara da cewar ” Ana shirya fim ne a matsayin labari wanda a ke so a fitar da wani sako daga karshe, amma shi labarin ba gaskiya ba ne, don haka sakon a ke so a isar.” Inji shi.

“Ni yanzu akwai abin da ko miliyan nawa za a ba ni a fim ba zan yi maka shi ba, ba Wai don kada a ce wani abu ba. Ni kaina tarbiyyar da iyaye na suka ba ni ya sa ba zan iya yi ba, don haka duk abin da na ke yi babu abin da ya kauce wa addini, amma su mutane kullum su na so ne a tsaya shekara da shekaru a waje daya ni kuma ba haka na ke ba ina da wayewa da kuma son ci gaba. Don haka duk masu son ci gaba su ne za su fahimci maganar da na ke yi. ” A cewar shi.

Labarai Makamanta