Ba A Cikin Fadar Shugaban Kasa Gobara Ta Tashi Ba – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi ƙarin haske da cikakken bayani game da rahotannin da ake yaɗawa cewa gobara ta tashi a fadar shugaban ƙasa ta Aso Villa Abuja, inda tayi mummunan ta’adi.

Fadar Shugaban kasan ta ƙaryata wannan labarin inda ta bayyana shi a matsayin labarin ƙanzon kurege da babu gaskiya a ciki, sai dai ana yaɗa shi ne domin wata ɓoyayyar manufa.

Mai magana da yawun Shugaban Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan, a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channel ya yi dashi dangane da yamaɗiɗin da ake yi na tashin gobarar.

Garba Shehu ya ƙara da cewa duk da an samu tashin wata wuta kusa da fadar Shugaban kasan amma ko kaɗan wutar bata shafi fadar ba, ana tsamanin wutar ta tashi ne sakamakon guntun karan sigari da wani mai wucewa ya jefar a kusa da wayar da ta zagaye ginin fadar.

“Da yammacin ranar Asabar 6 ga watan Maris, wuta ta tashi kuma ta ƙona yayi da ke tsakanin waya da kuma katangar da ta zagaye fadar Shugaban Kasa Villa, takamaimai tsakanin Villa da kuma Barracks da ke Asokoro,” in ji Garba Shehu.

Ya ce mutane da dama daga ciki da wajen Najeriya na ta bayyana damuwa game da rahoton gobarar, wanda ya ɓulla a wasu kafafen yaɗa labarai.

Ya ƙara da cewa nan take dakarun kashe gobara suka kashe wutar, wadda ta fara kuma ta ƙare a wajen ginin fadar.

Kazalika, ya ce ba a samu jikkata ko rasa rai ba kuma jami’ai na kan binciken musabbabin tashin wutar.

Labarai Makamanta