Ayyana ‘Yan Bindiga Matsayin ‘Yan Ta’adda Zai Dagula Lissafi – Gumi

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ayyana yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda kawai mataki ne da aka dauka na siyasa, wanda babu abin da zai canza illa dagula lissafi.

Malamin ya ƙara da cewar gwamnatin tarayya ta yarda wani sashi na kafafen watsa labarai a kasar suna juya ta yadda suka ga dama, yana mai cewa hakan ba zai kawo wani sauyi a kasa ba.

“Ina tunanin gwamnatin tarayya ta bari kafafen watsa labarai na wani yanki a kasar nan suna juya ta. “Ba zai kawo wani canji ba a kasa domin tun kafin a ayyana su dama ana yakar su ne kamar ‘yan ta’adda.”

Gumi, cikin sanarwar da hadiminsa Malam Tukur Mamu, ya fitar ya ce: “Wannan kawai suna ne kuma na yi imanin ba zai canja komai ba a kasa. “Idan ka tuna, IPOB ita ma an ayyana ta a matsayin kungiyar ta’addanci. Har takardan kotu ta tabbatar da haka, amma kasashen duniya ba su yarda da ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci ba.”

“Bai samar da sakamakon da ake bukata ba. Ba a hana su zuwa kasashen waje ba, suna nan a matsayin yan kasa. Wane irin ayyana wa ne wannan?.”

“Ina fatan ‘yan Nigeria ba za su dauki makiyaya a matsayin ‘yan ta’adda ba amma su dauka cewa akwai bata gari cikinsu idan aka kwatanta da nagari kamar yadda muka ke ganin harin IPOB kan hukumomin tsaro da wasu yan arewa a matsayin ta’addanci.

Kalilan cikin makiyaya ne ‘yan fashin daji idan ka duba adadinsu”Za a yi nadamar ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, masu ikirarin yin jihadi daga kasashen waje na iya shigowa Nigeria idan aka ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta