Ayar Dukan Mata Da Sarkin Waka Ya Dora A Shafinsa Ta Tada Kura

Labarin dake shigo mana yanzu haka daga Jihar Kano na bayyana cewar Fitaccen mawaki Nazir Sarkin waka ya janyo cece-kuce sakamakon wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram.

A ranar Litinin da yamma ne mawakin ya dauki hoton wani falle na wata aya daga cikin Al’Qur’an mai girma wacce ya yi tsokaci a karkashin hoton inda yace:

“Toh, ni dai naga ayar da tace mutum ya daki matarsa idan taci tura… Sai dai a taya ni nemo wacce tace kar a daki mata…nagode.”

Wannan wallafar ta sa mutane da dama suka dinga tsokaci suna sukarsa wasu na cewa alama ce da ke nuna yana dukan nashi matan. Duk da hakan akwai wadanda su ka dinga goyon bayansa su na cewa umarnin Allah ne. Akwai wadanda suke ganin ba haka ya kamata ya bayyana ba, kila ya yi wa ayar wata irin fahimta ta daban.

A yau kuma ya kara yin wani dogon bidiyo wanda yace haka ayar take kuma yana nan a kan bakarsa. Ya kara da cewa yana da matar da su ka kai shekaru 8 tare amma ko sasanta su ba a taba yi ba.

Don haka ba ya nufin a yi duka, kawai yadda ayar ta zo ne ya fassara ta. Ya hori maza da su guji dukan matansu saboda ba halayyar ta kwarai bane sannan mata su kasance masu bin dokokin mazajensu don gudun dukan.

A karkashin wallafar ya samu fiye da tsokaci dubu daya daga mutane daban-daban wadanda da dama su ka dinga sukar wannan fahimtar tasa.

Labarai Makamanta