Da Dumi-Dumi: Masu Biredi Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Kamfanonin biredi a Nijeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki sakamakon ƙarin farashin kayayyakin haɗi. Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito ƙungiyar ‘Association of Master Bakers and Caterer of Nigeria’ wadda ta ce farashin fulawa da sikari da sauran kayan haɗi da ake amfani da su wurin yin biredi duk sun yi tashin gwauron zabi. Ƙungiyar ta kuma ƙalubalancin gwamnatin Najeriya kan zargin nuna halin ko in kula dangane da wannan batu inda ƙungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki daga ranar 13 ga watan Yulin 2022. Ko a kwanakin…

Cigaba Da Karantawa

Adamawa: Hukumar NDLEA Ta Samu Gagarumar Nasara

A yayin da ake bikin ranan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya N D L E A shiya ta biyu wanda ya ƙunshi jihohin Adamawa Gombe da kuma Taraba tace ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi na dakile ayyukan shaye shaye a tsakanin Al umma. Kwamandan hukumar na Shiyar Alhaji Idris Muhammed Bello ne ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu a ofishin hukumar dake Yola. Idris Muhammed yace cikin nasarori da suka yi kawo yanzu sun…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Tashi Garin Mada

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Jama’ar Garin Mada na cigaba da tserewa daga garin bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a jiya. Shaidu sun tabbatar wa BBC cewa ƴan bindigan sun harbi mutum ɗaya sannan suka tafi da wasu mutum huɗu baya ga ɗumbin dabbobi da suka kora. Sai dai shaidun sun ce sojoji na dakatar da mutane da ke tserewa domin barin garin, inda suke hana su ficewa, lamarin da ya jawo mazauna Mada ke zanga-zanga. An tuntubi kakakin rundunar…

Cigaba Da Karantawa

IPMAN Za Ta Dakatar Da Kai Fetur Yankin Inyamurai

Ƙungiyar Masu Hada-hadar Fetur ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana cewa ba za su iya ci gaba da lodin fetur ana rarrabawa a cikin garuruwan yankin ƙabilar Igbo ba, wato Kudu maso Gabas a kan farashin da ake sayar da shi a yanzu. Manyan dillalan man sun tattauna ne da manema labarai a wata tattaunawa daban-daban da aka yi da su a Awka, ranar Juma’a. Sun ce idan wanda gare su yanzu a ƙasa ya ƙare, to ba za su ci gaba da raba fetur ɗin su na sayarwa ba. Rahotanni…

Cigaba Da Karantawa

Borno: APC Ta Kafa Kwamitin Sasanci

Jam’iyyar APC a Jihar Borno ta kafa wani kwamiti domin sasanta ƴaƴan jam’iyyar da ke da ƙorafe-ƙorafe bayan zaɓukan fitar da gwanin da aka gudanar a faɗin jihar. Shugaban jam’iyyar na APC a Jihar Borno Ali Bukar Dalori ne ya ƙaddamar da kwamitin a Maiduguri. Ya bukaci kwamitin ya ziyarci dukkan ƴan jam’iyyar da suka nemi yin takara a mukamai daban-daban amma ba su gamsu da sakamako zabukan ba. Baya ga lauya M.T. Monguno da Adamu, akwai kuma Mohammed Makinta, Alhaji Kaumi Damboa, Babagana Malarima, Sani Kuli Askira, Modu Kawu…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Kona Ofisoshin ‘Yan Sanda

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga su kai wani hari inda suka kona ofishin ‘yan sanda da gidaje a ƙauyen Zugu na ƙaramar hukumar Bukkuyum dake Jihar. Sai dai wani shugaban matasa a Bukkuyum ya shaida cewa babu wanda ya rasa ransa a sanadiyar harin kawo yanzu. Ya kara da cewa mazauna yankin sun tsere daga kauyukansu zuwa garin Bukkuyum da wasu ƙauyukan da ke cikin ƙaramar hukumar Gummi mai makwabtaka domin neman mafaka daga hare-haren. Sai dai kakakin rundunar…

Cigaba Da Karantawa

Dokar Zabe: Buhari Da Malami Sun Sha Kaye A Kotu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babbar Kotun Koli a ta yi watsi da karar da Buhari da Babban lauyan gwamnati suka shigar, suna bukatar fashin baki kan sashe na 84 na dokar zabe ta 2022. Sashen ya haramta wa duk wani mai rike da mukami na siyasa, da aka nada a dukkan matakai, ya kada kuri’a a zaben fitar da gwani na duk wata jam’iyya. Alkalan Kotun bakwai da suka yi zaman ranar Juma’a a karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dattijo, dukansu sun amince cewa karar yunkurin…

Cigaba Da Karantawa

Ta’addanci: Ana Wuce Gona Da Iri Wajen Kama Fulani – Gumi

Da ya ke magana a wurin taron kaddamar da Kungiyar Kare hakkin Makiyaya a Kaduna, Dr Ahmad Gumi ya ce kawo yanzu, akwai matasan fulani da yara da yawa a wadanda ba su ji ba ba su gani ba a tsare hannun jami’an tsaro. Ya ce dalilin kafa kungiyar shine tabbatar da cewa matasan Fulani da ba su aikata komai ba sun samu adalci, ya kara da cewa za ta taimaka wurin kawo zaman lafiya a kasar. “Kwanaki kadan da suka gabata, wani mutum ya kira ni ya ce jami’an…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Unguwannin Cikin Birni

Labarin dake shigo mana daga cikin garin Katsina na tabbar da cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai samame a wasu Unguwannin cikin birnin na Katsina. Wuraren da suka ƙaddamar da harin sun ƙunshi Sokoto Rima wajen Difiri, da bayan KTTV Inda ake kyautata zaton cewa sun Ɗauki Mutane Bakwai tare da tafiya dasu. Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbar da kai harin, Inda ya bayyana cewa Maharan sun kai samame ne da misalin ƙarfe biyu da rabi na…

Cigaba Da Karantawa

Korar Malaman Kaduna: Malamai Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kaduna ta kori malaman firamare sama 2000 a cikin makon jiya bisa dalilin basu zauna rubuta jarabawar kwarewa da gwamnatin ta shirya ba. Cikin waɗanda aka kora har da Shugaban kungiyar na kasa Mista Amba Audu wanda shima bai zauna rubuta jarabawar ba. Rahotanni sun bayyana Shugaban ƙungiyar ya umarci malamai da su kaurace wa jarabawar saboda babu dalilin sake rubuta irin wannan jarabawa bayan an taɓa rubuta irints a baya. Dalilin haka Shugaban Malaman ya ki rubuta jarabawar da wasu malamai sama…

Cigaba Da Karantawa

2023: Dalilin Da Ya Sa Ban Nemi Yin Tazarce Ba – Buhari

A ranar Alhamis ne mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana manyan dalilan da yasa bai zai sake tsayawa takara karo na uku ba, wato yin tazarce. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi magana ne a taron kungiyar kasashe renon Ingila da ya gudana a ƙasar Ruwanda. An gudanar da taron ne a cigaba da taron Shugabannin kasashen renon ingila wato Commonwealth karo na 26 a birnin Kigali na kasar Ruwanda. Mai girma Shugaban ƙasa ya nanata kudurinsa na mutunta iyakar wa’adin mulkinsa bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda…

Cigaba Da Karantawa

Neja: Jama’ar Gari Sun Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar mazauna yankunan da ta’addancin ‘yan bindiga yayi kamari a yankin Kusherki na karamar hukumar Rafi ta jihar sun nemi zaman lafiya da ‘yan bindiga. Rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindigan suka bukaci a yi yarjejeniyar zaman lafiya da mazauna yankin tare da sharadin cewa ba zasu dinga kai su kara wurin hukuma ba duk lokacin da suka ketare yankunansu. Shugaban yankin Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya sanar da Daily Trust cewa tuni suka tura wakilai domin tattaunawa da ‘yan bindigan.…

Cigaba Da Karantawa

Zargin Cire Sashin Mutum: An Damke Ekweremadu A Birtaniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar Hukumomi a kasar sun damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa. Hukumar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za’a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, kamar yadda jaridar Skynews ta ruwaito. ‘Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo…

Cigaba Da Karantawa

Zargin Tsafi: An Damke Sanata Ekweremadu A Birtaniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar Hukumomi a kasar sun damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa. Hukumar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za’a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, kamar yadda jaridar Skynews ta ruwaito. ‘Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Jami’an Tsaro Sun Tarwarsa Sansanin ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar tawagar hadin gwiwa da ta kunshi rundunar yan sandan Najeriya da yan bijilante a karamar hukumar Safana ta Jihar sun kashe yan ta’adda biyu yayin musayar wuta a kauyen Sabon Dawa. A cewar kakakin yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Laraba, ya ce an yi musayar wutan ne a yammacin ranar Talata, tsakanin ‘yan ta’addan da jami’an tsaro. “A ranar 21 ga watan Yunin 2021 misalin karfe 5 na yamma, an samu…

Cigaba Da Karantawa

Jira Ya Kare: Daliban Jami’a Za Su Koma Darasi – Minista

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce nan bada jimawa ba za a kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a ke yi a kasar. Ngige ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taro a fadar Shugaban kasa. Ngige ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na yin ko oho da korafe-korafen ASUU, inda ya tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugabancin kungiyar. Ministan ya kara da cewa…

Cigaba Da Karantawa

Sauya Sheka: Abdullahi Adamu Ya Koka Da Yadda Ake Barin APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar. Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023. Sanatocin da suka fice daga APCn sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina. Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Zai Ziyarci Kasar Ruwanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai halarci taron shugabannin ƙungiyar Commonwealth na ƙasashe rainon Ingila da ke gudana a ƙasar Rwanda daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni. Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Laraba ta ce shugaban zai halarci buɗe bikin a hukumance ranar Juma’a. Taron mai laƙabin CHOGM 2022, zai tattauna kan halin rayuwa da kuma ci gaban al’ummar ƙungiyar fiye da biliyan biyu da ke zaune a ƙasa 54 na nahiyoyin Afirka da Asiya da Amurka…

Cigaba Da Karantawa

Yakar Yunwa: Bankin Duniya Zai Ba Afirka Tallafin Dala Biliyan Biyu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Washington DC na ƙasar Amurka na bayyana cewar Bankin Duniya ya amince da tallafin kuɗi na sama da dala biliyan biyu ga ƙasashen Gabashi da Kudancin Afirka, don taimaka musu wajen bunƙasa wadatar abinci. A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce kimanin mutum miliyan 68 a yankin ke fuskantar matsalar ƙarancin abinci da barazanar yunwa. Ya ƙara da cewa matsalolin sauyin yanayi da tabarbarewar tattalin arziki da siyasa da rikice-rikice na kara ƙamari. Yaƙin Ukraine ya ƙara haifar da matsalar ƙarancin…

Cigaba Da Karantawa

Dalilinmu Na Kin Janye Tallafin Fetur – Fadar Shugaban Kasa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce abin da ya sa bai cire tallafin man fetur ba shi ne don gudun tsananta wa al’ummar ƙasar. Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Bloomberg ta intanet ta Amurka da aka wallafa a ranar Talata. Bloomberg ta tambayi Buhari cewa me ya sa ya ƙi amsa kiraye-kirayen da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da Babban Bankin Duniya ke masa tsawon shekaru na ya janye tallafin fetur kuma canjin kuɗaɗen ƙasashen waje su zama…

Cigaba Da Karantawa