Auren Danja Da Mansura Ya Zo Ƙarshe

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Mansura Isa ta bayyana cewa a yanzu haka babu aure a tsakaninta da mijinta Sani Musa Danja wanda ya ke fitaccen jarumi ne shi ma a masana’antar Kannywood.

An ruwaito Mansura Isan na bayyana hakan a shafinta na Instagram minti guda kafin ta goge rubutun.

A zantawar da mu ka yi da mijin nata, Sani Danja ta wayar salula, mun tambaye shi ko shin gaskiya ne sun rabu da matarsa Mansura Isah ? Sai ya amsa da cewa:”Ku je ku tambaye ta tunda ita ce ta rubuta”. Cewar Sani Danja.

Sai dai kuma wata majiya mai tushe wacce ta nemi mu sakaya sunanta ta tabbatar mana da cewa auren na Sani Danja da Mansura Isah ya daɗe da mutuwa yau tsawon shekara guda kenan ba sa tare a matsayin miji da mata.

Sani Danja da Mansura Isah fitattun jarumai ne masu tashe a masana’antar Kannywood waɗanda su ka yi aure irin na soyayya tsawon shekaru kusan goma da su ka gabata. Yanzu haka su na da ƴaƴa hudu mace ɗaya da maza ukku waɗanda su ka haifa tare kafin su kai ga datse igiyar auren da ke tsakaninsu.

An ce dalilin rabuwarsu na da alaka da auren sirri da Sani Danja ya yi a Kaduna ba tare da sanin Mansura ba har sai da matar ta haihu.

Majiyar ta ci gaba da cewa Mansura ta yi alkawari ba za ta ba shi ko daya daga cikin rayan ba.

Wadanda ke kusa da Mansura sun bayana cewa ba wannan ne farko da Sani Danja da Mansura suka rabu ba don ya taba sakinta a baya.

Mujallar Fim ta samu karin bayani da ke cewa Mansura ta gaji da halayen mijinta ne don saki mata hidimomin gida da ya ke yi inda ta ke daukar dawainiyyar tafiyar da al’amuran gidan.

Bincike ya nuna cewa Mansura dai mace ce mai kokarin neman na kanta da taimakawa marasa karfi.

Labarai Makamanta