Attajiran Duniya Bill Gates Ya Saki Matarshi

Mutumin da akayi ittifaƙin cewa ya fi kowa kuɗi a duniya Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da matakin da ya ɗauka na rabuwa da mai dakinsa Belinda.

Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.

Ma’auratan sun dade suna jagorantar ayyuka da dama na taimakon jama’a a sassan kasashen duniya daban-daban.

A cikin sanarwar da suka fitar na rabuwarsu, sun ce za su cigaba da aiki tare a gidauniyarsu na Bill and Melinda Gates Foundation.

Yayin aurensu na tsawon shekaru 27, sun haifi yara uku. “Bayan nazari mai zurfi da aiki kan zaman aurenmu, mun cimma matsayar kawo karshen auren,” a cewar sanarwar.

A cikin shekaru 27 da suka gabata, mun haifi yara uku sannan mun kafa gidauniya da ke ayyuka a sassan duniya domin inganta rayuwan mutane.

“Za mu cigaba da aiki tare domin cimma wannan manufar a gidauniyarmu amma ba za mu iya cigaba da kasancewa ma’aurata a yayin da za mu shiga matakai na gaba a rayuwarmu.

“Muna rokon a bamu sarari tare da mutunta sirrinmu a yayin da iyalin mu ke shiga wannan sabon rayuwar.”

Labarai Makamanta