Atiku Ya Koka Akan Yawan Satar Dalibai A Arewacin Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar Shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya jajantawa iyalan ɗalibai mata da aka sace a kwalejin zamanantar da gandun daji dake Afaka, unguwar Mando ta jihar Kaduna.

“Satar ɗaliban a Kaduna yazo bayan sati biyu da kuɓutar da ɗalibai mata 300 da aka sace a makarantar sakandiren mata ta gwamnati dake garin Jangeɓe dake jihar Zamfara wanda wasu ‘yan bindiga suka yi gaba dasu daga makarantarsu”.

“A shekarar 2014, Najeriya ta samu irin wannan matsalar, inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace ɗalibai mata sama da 200 a garin Chibok, dake jihar Borno. Har wane tsawon lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin?” Inji Atiku.

“Haka zalika a shekarar 2018, Boko Haram ta sake yin awon gaba da ɗalibai mata 110 a makarantar gwamnati dake Dapchi, jihar Yobe”.

Da yake magana akan lamarin a shafinsa na kafar sada zumuntar twitter, Atiku yace: “Abun damuwa ne matuƙa a wannan yanayi da muke ciki, wanda kullum ake harin sace ɗalibai mata a yankin Arewa.”

“Addu’a ta na tare da iyalan waɗanda abun ya shafa, kuma ina fatan babu wasu kuɗaɗe da za’a biya don ceto waɗannan yara.” Inji tsohon mataimakin shugaban ƙasan.

Atiku Abubakar ya ƙara da cewa: “Babban abin tambayan anan shine; har wane lokaci zamu ɗauka a cikin wannan yanayin?”

Labarai Makamanta