Atiku Ya Jinjinawa Buhari Kan Batun Sayar Da Matatun Mai

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi farin ciki tare da yaba wa Gwamnatin Tarayya kan matakin da za ta dauka na sayar da kadarorin kasar da suka hada har da matatun mai.

Waziri Adamawa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ya jima yana kiran a mayar da ragamar tafiyar da tattalin arziki ga ‘yan kasuwa.

A cewarsa, duk da a tsawon shekara ra’ayinsa ya sha bambanta da na gwamnatin APC, amma a yanzu ya gamsu da yadda gwamnatin ta dawo kan turbar da za ta kai kasar ga ci.

“Muradi na shi ne zaman lafiya mai dorewa da ci gaban Najeriya, zan yi farin ciki na bayar da shawarwari ga gwamnatin wannan zamani domin bunkasa kasarmu da al’ummarta,” in ji Atiku.

Labarai Makamanta