Atiku Ya Girgiza Da Rasuwar Mama Taraba


Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya jajantawa iyalan tsohuwar ministar mata Aisha Alhassan da ake kira Mama Taraba da Allah Ya yi wa rasuwa.

A ranar Juma’a aka sanar da rasuwar ‘ƴar siyasar ƴar asalin jihar Taraba.

Atiku ya ce rasuwarsa Aisha Alhassan ta matukar girgiza shi yana mai cewa, “na yi ƙoƙarin jin halin da take ciki da yamma bayan na kira lambarta ba a ɗauka ba! Inna lillahi wainna Ilaihi Rajiun!”

Haka ma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya Sana Bukola Saraki ya jajantawa iyalan Aisha Alhassan da abokai da kuma magoya bayanta.

Ya ce za a ci gaba da tunawa da iya saboda jajircewarta wajen yi wa jama’a aiki.

Marigayiyar ta wakilci Taraba ta Arewa a matsayin sanata, ta kuma rike mukamin ministar mata a gwamnatin Buhari.

A ranar Lahadi ake sa ran yin jana’izarta a garin Jalingo jihar Taraba.Article share tools

Labarai Makamanta