Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan Takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya Shilla Turai ana tsaka da gangamin yakin neman zabe.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bar kasar ne bayan ya gana da Asiwaju Bola Tinubu, ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC, a filin sauka da tashin jiragen Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja a yammacin jiya.
An samu rahotannin dake bayyana yadda ‘dan takarar jam’iyyar PDP ya bar kasar don neman lafiyarsa, amma sai dai Paul Ibe, mai magana da yawunsa, ya musanta hakan, tare da cewa Atiku ya yi tafiyar ne don kasuwanci.
“Tsohon mataimakin shugaban kasan ya fita kasar waje a daren jiya tare da abokan kasuwancinsa na daya daga cikin kasuwancinsa da ya samu tangarda saboda kullen Korona da rushewar tattalin arziki.” “Taron zai maida hankali ne wajen neman mafita akan yadda za’a bunkasa kayayyakin da kasuwancin da ake samarwa,”
You must log in to post a comment.