Atiku Ya Bada Shawarar Dawo Da Tsoffin Soji Bakin Daga

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar Atiku Abubakar ya yi kira da a kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Najeriya cikin gaggawa.

A wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce talakawan Najeriya na rayuwa cikin fargaba da ɗar-ɗar.

Ya ce babu inda ke da tsaro a ƙasar, ba a makaranta ba, ba a kasuwa ba, ba kuma a gonaki ba, ba masallatai ba kuma ba coci-coci ba

Atiku ya ce abin takaici ne yadda masu ta da ƙayar baya ke saɓaɓowa daga yankin arewa maso gabashin Najeriya suna shiga jihohi kamar jihar Neja wadda ke maƙwabtaka da babban birnin ƙasar.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar yi wa tsoffin jami’an tsaro kiranye su dawo bakin daga don taimakawa wajen yaƙi da masu ta da ƙayar baya.

Atiku ya ce Najeriya za ta iya koyi da ƙasashe kamar Lebanon da Liberia da Saliyo da suka yi wa tsoffin sojojinsu kiranye kuma suka amsa don yi wa ƙasarsu hidima.

Sannan ya shawarci gwamnatin tarayya kan ƙara wa jami’an tsaro albashi inda ya ce hakan zai ƙara masu ƙwarin gwiwar yin yaƙi bin haƙƙi da gaskiya.

Labarai Makamanta