Atiku Shirgegen Makaryaci Ne – Tìnubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ta APC Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana babban abokin takararsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a matsayin mayaudari kuma Maƙaryaci wanda ke yi wa ‘yan Najeriya romon baka.

Bola Tinubu, wanda ya bayyana haka a taron majalisar dokokin yankin Kudu-maso-Kudu a ranar Talata a Calabar, ya zargi Atiku da sauran ’yan takarar da zage-zage ba tare da hujja ba.

“Wadanda suka ce suna takara ba su da gaskiya a cikin su; ba za su iya cika alkawuransu ba; duk abin da suke sha’awar shi ne su zage ni, amma duk da haka, ba su da gaskiya,” in ji Tinubu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply