Atiku Ba Ɗan Najeriya Bane Bai Cancanci Yin Takara Ba – Malami

Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce abin da ya tabbata akan tsohon mataimakin Shugaban ƙasa Atiku shine shi Baƙon haure ba ɗan Najeriya ba, saboda haka dokar kasa ba ta bashi damar neman Shugabancin kasa ba.

Malami ya yi rantsuwa a kan cewa iyayen Atiku mutanen Kasar Kamaru ne, kuma a yankin kasar Kamaru aka haife shi, bisa ga dokar kasa bata bashi damar fitowa takarar Shugabancin ƙasa ba.

A cewar Ministan shari’an, idan aka bar Atiku Abubakar ya fito takara, an saba wa sashi na 25(1), (2) da kuma sashe na 131(a) na dokar kasa dokar zabe na kasa.

An ruwaito cewa Ministan Shari’an ya kai wannan magana ne gaban babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

Abubakar Malami ya fallasa salsalar Atiku Abubakar data koreshi daga zama ɗan Najeriya, ya roki Alkali ya duba yadda aka haifi Atiku Abubakar, ya hana shi tsaya wa takarar shugabancin Najeriya.

Tun kafin zaben 2019 ne Lauyoyi babban Lauyan gwamnatin tarayyar a karkashin Lauya Oladipo Okpeseyi su ka shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, da har yau ba a saurara ba.

Rahotanni sun bayyana cewa za a zauna game da wannan shari’a a ranar 4 ga watan Mayu, 2021.

Ministan shari’ar ya kafe a kan cewa an haifi Atiku ne a shekarar 1946 a garin Jada, a wancan lokaci wannan yanki na Jada ya na cikin Arewacin Kamaru, kafin ya shigo Najeriya.

Sai a 1961 ne aka dawo da Jada cikin Najeriya, don haka Malami ya ce Atiku bai da hurumin da zai nemi kujerar shugaban kasa domin shi ba haifaffen Najeriya ba ne.

Ministan ya ce har iyayen tsohon mataimakin shugaban kasa su ka bar Duniya, su ba ‘yan Najeriya bane.

Kwanaki Adamu Atiku-Abubakar, ‘dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce mahaifinsa zai sake fitowa takarar shugaban kasa.

Alhaji Adamu Atiku-Abubakar wanda Kwamishina ne, ya bayyana wannan ne sa’ilin da ya ke bayani a game da nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a jihar Adamawa.

Labarai Makamanta