Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar a ranar Talata, ta ce ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko wata kungiya na toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja da sunan zanga-zanga ba.
Kwamishinan tsaro na cikin gida a jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce ba za a amince da wannan matakin ba, kuma wani share fage ne na karya doka da oda.
“Da wannan sanarwar, ana shawartar mutane ko ƙungiyoyin da ke shirin hana zirga-zirgar ’yan ƙasa domin nuna damuwa akan yajin aikin ASUU da su daina don samun zaman lafiya.
“Duk da cewa gwamnatin jihar Kaduna ba ta hana ‘yan kasa ‘yancin fadin albarkacin bakinsu ba, ya zama dole ne a rika kula da harkokin tsaro da tsaron jama’a a kodayaushe.
“Haɗarin toshe hanya mai mahimmanci kamar hanyar Kaduna zuwa Abuja ba shi da wani amfani idan aka duba halin da ake ciki na tsaro da suka shafi hanyar da sauran wurare.” “Dole ne a mayar da hankali sosai kan yiwuwar wasu tarukan da zasu iya rikidewa zuwa tashin hankali.
“Don haka ana shawartar ‘yan kasa da su guji haifar da irin wadannan cunkoson, musamman wadanda za su yi tasiri ga al’amuran zamantakewa da tattalin arziki na sauran ‘yan kasa, ko kuma jefa rayuka cikin hatsarin da ba dole ba.
You must log in to post a comment.