Asiri Ya Tonu: An Gano Ma’aikatan Gwamnatin Zamfara Da Hannu A Ta’addanci

Rahotanni daga Gusau Babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar an bankado wasu ma’aikatan gwamnati da ake zargin cewa suna da hannu dumu dumu a ayyukan ta’addanci da ya addabi Jihar da yankin Arewa gaba ɗaya.

A cewar wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Magaji Dosara ya sanyawa hannu, ma’aikatan na cikin mutum 35 da aka kama a Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnatin ta bayyana mamaki kan yadda wasu daga cikin mutanen da aka kama suka kasance ma’aikatan gwamnati.

A cewar sanarwar, tuni aka yi bincike a kan mutanen inda kuma suka tabbatar da yadda suke ba da gudummawa wajen aikata miyagun laifuka.

Labarai Makamanta