Arewa Maso Yamma Na Fama Da Gagarumar Matsalar Rashin Lafiya – Likitocin Duniya

Kungiyar likitocin duniya ta Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ce arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar gagarumar matsalar kiwon lafiya.

Kungiyar ta ce kananan yara masu dimbin yawa suna fuskantar matsalar tamoiwa.

MSF ta bayar da kulawa ga kananan yara 100,000 da ke fama da tamowa tun daga farkon shekarar nan, tana mai cewa kimanin yara 17,000 suna bukatar kulawar asibiti.

Kungiyar ta kara da cewa taimakon da ake bai wa yaran ya yi matukar kadan, domin kuwa an mayar da hankali kan yankin arewa maso gabashin kasar inda ake fama da rikicin Boko Haram.

Labarai Makamanta

Leave a Reply