APC Zata Yi Babban Kamu Daga Jihar Bauchi – Zulum

Mai girma Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, yace nan bada jimawa ba jam’iyyar su ta APC za ta yi wani babban kamu a Jihar Bauchi wanda zai ba jama’a mamaki.

Gwamna Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin bikin saka harsashin sabon gagarumin gidan gwamnatin jihar Bauchi da zai lamushe N6.3 biliyan.

“Bari in sake nuna godiyata ga takwarana gwamnan jihar Bauchi da sauran takwarorina na arewa maso yamma da suke bani goyon baya mai matukar yawa.

“Rikici daya da nake yi da takwarana gwamnan jihar Bauchi shine kin dawowa jam’iyyar APC. Da izinin Allah nan babu dadewa zai dawo cikinmu. Ina goyon bayan shi,”.

Zulum wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso gabas yayi bayani a kan cigaban da yankin arewa maso gabas ke samu. Ya ce kungiyar tayi matukar kokari wurin sauya alkiblar yankin a watanni kalilan bayan kafa ta kuma zata cigaba da samar da sauye-sauye.

Ya kara da sanar da cewa kungiyar na tunanin kafa bankin arewa maso gabas wanda zai dinga samar da kudade ga kananan sana’o’in matasa, mata da masu kananan karfi.

Labarai Makamanta