APC Za Ta Ladabtar Da Sanatocin Dake Tirjiya Ga Gwamnoni

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, yana fusakantar matsin lamba a game da zaben shugabanni da aka gudanar.

Wani rahoto da muka samu ya bayyana cewar an taso Mai Mala Buni a gaba, ana so ya hukunta wasu daga cikin ‘yan jam’iyya da suka shirya zaben taware a APC. A dalilin rikicin da ake fama da shi tsakanin wasu jagororin APC na kasa da gwamnonin jihohinsu, ‘yan taware sun ja daga a zaben shugabannin jihohi.

Wani daga cikin gwamnonin jihar da aka samu shugabanni fiye da daya, ya taso uwar jam’iyya a gaba, yana so a hukunta wadanda suka raba kan ‘yan jam’iyya. An samu irin wannan rigima a Kano, Legas, Ogun, Kwara, Osun, Filato, Neja, Akwa Ibom, da Enugu.

Daga cikin wadanda ke kan gaba wajen goyon bayan wadanda ake ganin ‘yan taware akwai Ibrahim Shekarau (Kano), da kuma Ibikunle Amosun (Ogun). Har ila yau akwai irinsu Rauf Aregbesola (Osun), Sanata Rochas Okorocha (Imo), Akinwunmi Ambode (Lagos), da Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom).

A jihar Osun, bangaren Rauf Aregbesola sun kai kara kotu a game da zaben da aka shirya. Hakan ya saba wa umarnin da shugabannin jam’iyyar APC suka yi. Wata majiya tace gwamnoni na so a hukunta masu ja da su domin a koya wa wasu hankali yayin da ake shirin gudanar da babban zaben shugabanni na kasa.

Labarai Makamanta