APC Ta Tsawaita Wa’adin Zabukan Fidda Gwani

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyya mai mulki, APC ta ƙara wa’adin ranakun zaɓukan fidda-gwanin takarar gwamnoni, sanatoci, wakilan tarayya da na jihohi.

Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyyar Suleiman Argungu ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Da fari an shirya za a yi zafin fidda-gwanin gwamnoni a ranar 18 Ga Mayu, shi kuma na Majalisar Jihohi a ranar 20 Ga Mayu, za a yi na Majalisar Tarayya a ranar 22 Ga Mayu, na Sanatoci kuwa a ranar 24 Ga Mayu.

Amma a yanzu sanarwar ta nuna za a yi zaɓen fidda-gwanin takarar gwamnoni a ranar 20 Ga Mayu, na Majalisar Dokokin Jihohi kuwa ranakun 22 Ga Mayu.

Zaɓukan fidda-gwanin Sanatoci zai wakana ranar 24, sai kuma na Majalisar Tarayya kuma a ranar 25 Ga Mayu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply