APC Ta Tsawaita Wa’adin Shugabancin Kwamitin Riko Na Jam’iyyar

Labarin da ke shigo mana da duminsa a yanzu na nuna cewa majalisar zartaswar jam’iyya mai mulki ta APC, ta tsawaita wa’adin kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

An ruwaito cewa an tsawaita wa’adin zuwa ranar 30 ga Yunin 2021.

Hakan ya faru ne a ganawar gaggawan da majalisar tayi ranar Talata a fadar shugaban kasa dake Aso Villa Abuja.

An gudanar da taron ne karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Tun da fari dai sai da Majalisar zartawas ta rushe dukkanin shugabancin jam’iyyar da ke jihohi da Shiyyoyin ƙasar baki ɗaya.

AMatakin da Majalisar zartawas ta ɗauka na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun sauya sheka a tsakanin ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa ga Jam’iyya mai mulki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply