APC Jam’iyyar Mashaya Ce – Gwamnan Binuwai

Biyo bayan cece-kucen da ya biyo bayan kalaman da ya yi kan wasu ‘yan jiharsa da ya bayyana a matsayin ‘yan barasa, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi karin haske akan kalaman nashi.

Gwamnan Ortom ya bayanin ne a lokacin da yake kaddamar da sabon ginin Cocin Embassy na RCN a Makurdi, babban birnin jihar Benue, gwamnan ya ce wasu ‘yan jiharsa ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke wuni suna shan barasa suna ci gaba da cin mutuncinsa.

Da dama dai sun bayyana hakan a matsayin abin da bai kamata ba, inda suka soki gwamnan da kuma zarginsa da rashin mutunta ‘yan jihar. Sai dai a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Nathaniel Ikyur ya fitar a madadin sa, gwamnan ya ce batun nasa tsokaci ne ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a Benue.

Labarai Makamanta