APC Jam’iyyar Marasa Imani Ce – Sule Lamiɗo

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta APC bata da hangen nesa, tausayi da imani da kuma jin kai, wanda wannan shine babban dalilin daya sanya kasar da jama’arta suka shiga cikin wani mawuyacin hali na tsaka mai wuya.

Da ya ke jawabi yayin kaddamar da aikin titin Rumuji, Ibaa, Obelle Isokpo a karamar hukumar Emouha ta jihar Ribas, a ranar Litinin, Lamido ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin tarin mutane da ke cike da fushi, hassada da gaba.

Lamiɗo ya kara da cewar ayyukan sake fasalin filayen jiragen sama, farfado da layyukan dogo da sauye-sauyen da wannan gwamnatin ke alfahari da su duk ayyukan da jam’iyyar PDP ta kirkira ne.

“A lokacin da suka samu mulki, ba su da shirye-shirye. Ba su da tsari; abinda suka sa a gaba kawai shine su kori gwamnatin PDP saboda muna aiki; muna da tsari, saboda muna aiki tukuru, saboda muna da tausayin mutane,” in ji shi.

“Su APC ba za su iya tunani ba. Ba su da hangen nesa, ba su da tausayi, kawai mulki suke nema kuma yanzu mulkin na wahal da su, saboda ba su rike amanar mulkin ba.”

Tunda farko, Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya ce yana gudanar da ayyukansa ne domin samar da kyakyawar yanayi da jama’ar jiharsa za su amfana da shi su nemi arziki su bunkasa.

Labarai Makamanta