APC Da PDP Sun Soki Goyon Bayan Obasanjo Ga Peter Obi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jam’iyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyar hamayya ta PDP ,sun mayar da martani ga tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo game da maganar da ya yi na cewa ya na kira ga matasan Najeriya da su goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar Labour Peter Obi.

Kalaman dai na tsohon shugaban Najeriya, Chief Olusegun Obasanjo ya yi, na cewa, ya na kira ga matasan Najeriya da su goyi bayan Peter Obi, bisa ga dukkan alamu bai yi wa manyan jam’iyun biyu dadi ba.

Babban daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ƙasa na jam’iyyar APC Bala Ibrahim ya shaida wa BBC cewa maganar Obasanjon ba wani abun damuwa ba ne domin ba wata magana ba ce sabuwa.

”Bana so in ƙaskantar da matsayin Obasanjo da martabarsa da darajarsa a matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa, amma gaskiyar magana ita ce Obasanjo ya zama mushen gizaka ne yara kawai yake bai wa tsoro, amma baya wani tasiri a abubuwan da yake yi” in ji Bala.

Ya ƙara da cewa Obasanjo ko akwatinsa ma baya kawowa, ballantana ƙasa ba ki ɗaya. Sannan kuma ya ce dama Obasanjon ya saba da irin wannan kira a baya kuma kiran nasa baya wani tasiri.

Daga nata ɓangaren ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta bakin Sanata Ibrahim Tsauri mamba a kwamitin dindindin na jam’iyyar ya ce tsohon shugaban ƙasar na fama da gigin tsufa.

Labarai Makamanta