Shirin rushe tsohuwar kasuwar Panteka da ke kan titin Enugu a kusa da Kwalejin Kimiyya da fasaha da ke Kaduna da El Rufa’i ya ɗaura aniya, ta ci gaba da tsorata ‘yan kasuwar da duk wasu masu samun abin masarufi daga kasuwar.
Wannan rade-radin ya tada hankalin Maƙera da sauran masu saye da sayarwa da ke wurin. Tsoronsu ya sake yawaita tun bayan da aka rushe fitacciyar Kasuwar Barci wacce take da kusancin kilomita kalilan daga gare su.
Kasuwar ta yi shekaru masu yawa da kafuwa kuma ta samo sunanta ne daga wata mata mai suna Panteka, wacce ke hada tukwanen karfe tana sayarwa a tsohon sashin kassuwar da ake kira da ‘Yantinka.
A matsayin babbar kasuwar karafuna a Najeriya wacce ta kware a kere-kere, tsohuwar kasuwar Panteka na da sassa 40. Kowanne sashi na da abu daya da makeran yankin suka kware a kerawa.
Kasuwar ta kasance babban wurin horar da dalibain Polytechnic ta Kaduna tare da sauran manyan makarantu a fadin arewacin Najeriya.
Cike da tsoron rushe kasuwar, shugaban Kwalejin Kimiyya da fasaha, Farfesa Idris Bugaji, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta sake duba wannan hukuncin nata.
A maimakon rushe kasuwar, ta mayar da ita wani wurin tarihi sakamakon tsohon tarihin da kasuwar ke da shi a yankin arewacin Najeriya. Farfesa Bugaje ya ce, “Ina so in yi amfani da wannan damar wurin kira ga Gwamna Nasir El-Rufai da ya mayar da Kasuwar Panteka ta zama wurin tarihi. Kada a rusheta, a mayar da ita wurin tarihi a jihar.”
Shugaban Kwalejin ya kara da cewa, “Idan ana son yin sabon gini, a bar tsohuwar Kasuwar Pantekan. Zai yi kyau idan aka gyara kasuwar tare da inganta sannan a mayar da ita wurin tarihi.”
Ya tabbatar da cewa, rushe kasuwar zai durkusar da makera da masu saide-saide a kasuwar tare da jefa makarantar da ke da makwabtaka da ita cikin wani mawuyacin hali.
You must log in to post a comment.