Ana Satar Danyen Mai Na Dala Miliyan 700 Duk Wata A Najeriya – NNPC

Babban Manajan Kamfanin NPMS, reshe daga kamfanin fetur na ƙasa, NNPCL, Bala Wunti, ya ce a duk wata ana satar ɗanyen mai aƙalla ganga 470,000 a ƙasar nan.

Wunti ya yi wannan bayani lokacin da ya ke rangadin duba kadarorin NNPCL.

Ya ce an ƙiyasta ɗanyen man da ake dacewa ɗin duk wata zai kai na dala miliyan 700.

Sannan ya ce rabon da bututun mai na Bonny Terminal ya yi aiki tun cikin watan Maris, saboda ɓarayin ɗanyen mai masu fasa bututu.

Ya ce wannan matsala ta haifar wa Najeriya ƙarancin kuɗaɗen shiga, kawo cikas wajen raba man gas da kuma haifar da ƙarancin ɗanyen man da ake haƙowa.

Haka a ƙarshen watan Agusta shi ma Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce da haɗin-bakin mutanen yanki, shugabannin addinai da jami’an tsaro ake satar ɗanyen mai.

Labarai Makamanta