Gwamnatin Kenya ta buƙaci ƴan ƙasar su yi amfani da wasu hanyoyi yayin da ake fama da ƙarancin kwaroron roba.
An bayyana cewa ƙasar na fama da ƙarancin kwaroron roba, inda alƙalumma suka nuna cewa kwaroron miliyan 1.6 gwamnati ta samar maimakon miliyan 455 da ya kamata a samar a shekara.
A cewar Star Kenya, wani rahoto da asusun yaƙi da cutar AIDS da tarin fuka da maleriya ya nuna cewa kwaroron roba miliyan 20 aka raba a ƙasar.
Jaridar ta ambato ma’aikatar lafiya ta ƙasar na cewa gwamnati za ta yi ƙoƙarin magance matsalar fatarar ƙwaroron roba da ake yi a ƙasar.
Lamarin dai ya haifar da muhawara musamman a kafofin sadarwa na intanet, saboda yadda wasu ke la’akari da manufar amfani da kwaroron roba domin kare cutuka da kuma hana ɗaukar ciki.
Rahotanni dai sun nuna cewa an samu ƙarancin ne sakamakon haraji da gwamnati ta saka wa kayayyaki.
You must log in to post a comment.