Ana Damfarar Mutane Da Sunana – Shugaban NNPC

Shugaban babban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Mele Kyari, ya ja hankalin jama’a da su guji yin mu’amala da wasu ‘yan damfara da suka bude shafukan Facebook da sunansa.

Malam Kyari ya ce ‘yan damfarar suna amfani da sunansa inda suke kwadaita wa mutane cewa yana bayar da bashi na gudanar da aikin gona.

“Ba ni da wani shafi a Facebook. Akai shafuka da dama a Facebook da aka bude da sunana, amma ba ni da ko daya. Ku kiyaye da ‘yan damfara,” in j Mele Kyari.

‘Yan damfarar intanet dai suna amfani da sunayen manyan jami’an gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin damfarar jama’a.

Labarai Makamanta